An yi gyara a kasafin kudin Najeriya

Bukola Saraki tare da shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption A baya dai an yi rade-radin kasafin kudin ya yi batan dabo.

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa ta aikewa majalisar dokokin kasar wasika kan wasu sauye-sauye da aka yi a kasafin kudin wannan shekarar.

A kwanakin baya ne dai akai ta rade-radin kasafin kudin ya yi batan dabo, labarin da fadar shugaban Najeriyar ta musanta.

Mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin majalisar wakilai Abdurrahman Kawu Sumaila, ya shaidawa BBC cewa babu abinda ya sauya na yawan kudin da aka ware a kasafin bana.

Ya kuma musanta batun da ake yi na shugaban kasar ya warewa fadarsa makudan kudade alhalin 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali.

Kawu Sumaila ya kara da cewa an yi sauye-sauyen ne akan wasu ma'aikatu da aka rage kudaden da aka ware musu, aka kara a wasu ma'aikatun da suke bukatar kudade da yawa.