IS na garkuwa da mutane dari hudu a Syria

Garin Deir El -Zour Hakkin mallakar hoto Reuters

Masu fafutika na Syria sunce yan gwagwarmayar kungiyar IS sun yi garkuwa da fararen hula fiye da dari hudu a lokacin wani hari a bayan birnin Deir al -Zour.

Mutane akalla dari da talati ne aka kashe a wani farmaki na kungiyar ta IS a kan yankunan da gwamnati ke rike da su.

Da yawa daga cikin wadanda aka kashe din ko kuma aka yi garkuwa da su dangi ne na mayakan dake mara wa gwamnati baya.

Kafofin watsa labarai na gwamnatin Syria sun bayar da rahoton cewar mutane dari ukku ne aka kashe, da yawansu mata da kananan yara, inda aka fille wa wasu kawuna ko kuma aka gicciye su.

Kungiyar dake sa ido kan lamuran kare hakkin bil adama a Syria ta ce mai yiwuwa an dauki mutanen da aka yi garkuwar da su zuwa hedikwatar kungiyar ta IS a Raqqa.