BBC ta gano cuwa-cuwa a wasannin Tennis

BBC da kafar yada labarai ta BuzzFeed sun samu wasu takardu na bayanan sirri da ke nuna an yi coje wajen hada wasu manyan wasanni na tennis, ciki har da gasar Wimbledon.

A shekaru 10 da suka gabata, an yi ta kai korafin 'yan wasan tenni 16 da suke cikin shahararrun 'yan wasa 50, a gaban kwamitin da'a na gasar tennis, bisa zarginsu da bari a yi nasara a kansu da gangan.

Dukkan 'yan wasan kuma, da suka hada da wadanda suka lashe kyaututtuka na Grand Slam, sun ci gaba da shiga wasanni a gasar.

Kwamitin da'a na gasar tennis, wanda aka kafa domin ya tsaftace gasar, ya ce ba ya lamuntar duk wani abu da ke da alaka da rashawa.

Takardun da BBC da Buzzfeed suka samu sun hada da sakamakon wasu bincike-bincike da hukumar shirya wasannin tennis ta sa aka gudanar a shekarar 2007.

A wani rahoto na sirri da aka gabatar wa hukumomin shirya wasanni tennis a 2008, kwamitin binciken ya bukaci a binciki wasu 'yan wasan tennis 28, amma aka yi biris da batun.