Macizai sun takura wa masu yawon bude-ido

Hakkin mallakar hoto abc
Image caption Mesa

Wasu macizai sun hana masu yawon bude-ido rawar-gaban-hantsi a Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina, har ta kai ga an rufe fitattun wuraren shakatawa da ke bakin teku, saboda mamayar da macizan suka yi, wadanda aka ce suna da dafin gaske.

Mahukunta dai sun ce macizan kan nade ne a jikin ganyen bado, wanda ambaliyar ruwa ta share daga cikin kogi zuwa waje a arewa-maso-gabashin kasar.

An dai gargadi masu yawon bude-ido da su guji yin wanka da kafa gadajen shan hantsi a bakin teku a yankin.

Kazalika ruwan ya tura wasu muggan namun dawa zuwa gabar ruwa, ciki har da Alhanzir.