Biritaniya za ta koya wa mata Musulmai Ingilishi

Image caption Biritaniya ta soki maza Musulmai a kan mata.

Gwamnatin Biritaniya za ta kashe fiye da dala miliyan 28 domin karfafa gwiwar mata Musulmi su koyi turanci.

Hakan dai na cikin shirin gwamnatin na samar da al'uma mai inganci da kuma rage kaifin masu tsattsauran ra'ayin addini.

Firai Ministan Biritaniya David Cameron, wanda ya bayyana hakan a wata wasika da ya wallafa a jaridar The Times, ya zargi Musulmi 'yan tsiraru da abin da ya kira "halayen da ke kawo koma-baya", yana mai cewa suna yin illa ga dubban mata Musulmai wadanda ke amfani da harshen ingilishi.

Ya kara da cewa dole ne Biritaniya ta dauki kwararan matakai domin jaddada dabi'unta masu sassauci.