Za a rufe shafin abotar Reunited

Image caption Friends Reunited

Friends Reunited, daya daga cikin shafukan abota na intanet da ke Birtnaiya zai rufe shafinsa.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiri shafin, Steve Pankhurst ya bayyana cewa har yanzu wasu daga cikin ma'abota shafi na amfani da shi, amma a cewarsa an saba wa akidar da aka bude shafin dominta.

A shekara ta 2000 ne dai aka bude shafin, kuma gidan talabijin na ITV ne ya saye shi a shekara ta 2005 a kan fam miliyon 250.

Sai dai shafin ya gaza wajen gogayya da sauran shafuka takwarorinsa a dandalin sada zumunta.

Mr Steve Pankhurst ya ce galibin masu shiga shafin kan shiga ne kawai domin su tura wasu sakonninsu, kuma mafi yawan am'abota shafin miliyon goma sun bude ne tun sama da shekara 10 da suka wuce, sannan bayanai ko tarihinsu ya tsufa ba tare da an sabunta ba.

Wata matsalar ita ce har yanzu an kasa fitar da jarin da aka zuba ballantana a ci riba.

Mr Steve Pankhurst ya ce "abin bakin ciki ne, ina ganin cewa ya kamata a binne Friends Reunited a yi gaba"

ya kara da cewa yana shirin bude wani sabon shafi mai suna Life, inda ma'abota za su dinga ba da labarin wasu muhiiman al'amuran da suka faru a rayuwarsu.