An soma bayar da abinci ga dalibai a Kaduna

Image caption Gwamna El-Rufai ya ce shirin zai shafai daukacin daliban jihar

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta kaddamar da shirin bayar da abinci kyauta ga dalibai a makarantun firamare da ke fadin jihar.

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ne ya kaddamar da shirin a wata makarantar firamare ta gwamnati da ke Barnawa a karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

A jawabinsa a bikin kaddamar da shirin, El-Rufai ya ce matakin na daga cikin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa a bara.

Ana sa ran dalibai kusan miliyan biyu ne za su ci gajiyar shirin bayar da abincin na gwamnati.