Sojoji na farautar masu fasa bututan mai

Image caption A shekara ta 2009 wasu daga cikin mayakan suka ajiye makamansu a Niger Delta

Jami'an tsaron Najeriya sun ce su na farautar masu tayar da kayar baya da suka kai hare-hare a kan bututan mai a yankin Niger Delta a karshen mako.

Rahotanni sun ce tsaffin mayaka daga yankin mai arzikin man fetur da ake zargin suna biyayya ga tsohon madugunsu, Government Ekpemupolo, wanda ake kira 'Tompolo', su ne suka kaddamar da hare-hare a kan bututan mai.

Ana zargin an kai hare-haren ne saboda nuna adawa da sammacin da kotu ta bayar na a kama Tompolo.

Sai dai masu tayar da kayar bayan sun musanta zargin hannu a hare-haren.

Ana zargin Tompolo da karkatar da Naira biliyan 34 a wata kwangila ta tsaro domin kare bututan mai a yankin Niger Delta, ko da yake ya musanta zargin.

Tompolo ya kasance daya daga cikin shugabannin masu tayar da kayar baya a yankin mai arzikin man fetur, kafin ya amince da yarjejeniyar afuwa da gwamnati ta yi musu a shekara ta 2009.