An killace mutane 109 a kasar Saliyo

Jami'in lafiya a bakin aiki Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar Ebola ta hallaka mutane 4000 a kasar saliyo kadai.

Kasar Saliyo ta zakulo wasu mutane sama da dari da ake ganin cewa watakila sun yi mu'amala da wata mata da cutar Ebola ta halaka a makon jiya.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce an kebe mutum 28 daga ciki don sa-ido a kansu.

Haka ma'aikatar lafiyar ta ce ba a binne gawar matar yadda ya kamata ba.

An dai samu labarin mutuwar matar ne kwana daya, bayan Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa an yi nasarar yakar cutar Ebola a shiyyar Afirka ta yamma.

Kusan mutum dubu hudu ne cutar ta halaka a kasar Saliyo.