Kun san halin da attajirai suka jefa talakawa?

Kungiyar agaji ta Oxfam ta ce dukiyar da kashi daya cikin dari na attajiran duniya, watau mutane miliyan 73 suka mallaka, ta haura dukiyar da sauran jama'ar duniya ta mallaka idan aka hade ta wuri guda.

Wani sabon rahoton kungiyar ta Oxfam a kan rashin daidaito tsakanin al'umomin duniya, ya yi kiyasin cewa dukiyar da mutane 62 da suka fi kowa arziki a duniya suka mallaka, ta kai adadin arzikin da rabin talakawan duniya biliyan uku da miliyan dari uku suka mallaka.

Kungiyar agajin ta ce attajirai a duniya sun boye arzikinsu na kusan dala tiriliyan bakwai da rabi a kasashen da ba sa biya musu haraji, don hake ne kungiyar Oxfam ta yi kira ga gwamnatoci da su dauki mataki a kan masu zamewa biyan haraji.

Attajirai a Afirka su ke da dala biliyan 500 daga cikin dukiyar da ke boye a kasashen da ba a biya musu haraji, kuma hakan ya na janyo wa nahiyar Afirka asarar kudin shiga da ya kai dala biliyan 14 duk shekara.