An dakatar da gidajen rediyo 21 a Tanzania

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rediyo na da matukar farin jini a Afrika

Hukumar kula da sadarwa ta kasar Tanzania ta dakatar da lasisin gidajen talabijin shida da na gidajen rediyo 21 saboda rashin biyan kudin haraji na gwamnati.

Hukumar ta ce ta tunatar da tashoshi 40 a cikin watan Yulin bara kan batun bashin da ake bin su, amma kuma guda 13 ne suka biya kudin harajin.

A kan haka ne aka janye lasisin tashoshi 27, har sai sun biya kudaden da ake bin su.

Sai dai cibiyar kafafen yada labarai a Tanzania ta soki matakin, inda ta ce zai taka 'yancin mutane na samun bayanai.

Sakataren cibiyar, Kajubi Mukajanga ya ce dakatar tashoshin watsa labarai, tamkar hana mutane samun labarai ne masu mahimmanci.