"Sojoji sun kashe 'yan Shi'a da dama"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Shi'a na yin muzahara domin ganin an saki shugabansu.

Wasu ganau sun tabbatar wa BBC cewa sojojin Najeriya sun halaka 'yan kungiyar Shi'a da dama lokacin da suka kai samame a Hedkwatar kungiyyar da kuma gidan shugabansu a watan jiya.

Wakilan BBC, wadanda suka kai ziyara a garin Zaria, sun tattauna da mutane da dama wadanda suka ga yadda aka yi artabu tsakanin sojojin da 'yan Shi'a.

Wani matashi dan kimanin shekara 16 da ke Hedkwatar kungiyar, watau Hussainiya, wanda kuma BBC ta taras a gadon asibiti, ya ce sojoji ne suka harbe shi, yana mai karawa da cewa, "sojojin sun yi ta harbin mutane, kuma ni kaina na ga gawarwakin mutane arba'in".

Rundunar Sojin Najeriya dai ta musanta cewa an take hakkin bil'adama, ta kuma ce ana ci gaba da bincike domin tabbatar da yawan mutane da suka rasa rayukansu a rikicin.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce daruruwan mutane ne suka mutu a fito-na-fiton da aka yi a garin Zariya.