Ayatollah bai yi murna da dage takunkumi ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ayatollah ya shawarci shugaban Iran da ya yi taka tsantsan da Amurka

Jagoran addinin Kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, bai yi farin ciki da dage takunkumin kasa da kasa da aka yi wa kasarsa ba, game da shirinta na Nukiliya.

Gidan Talabijin na kasar ya ruwaito jagoran addinin yana gargadin cewa dole ne Shugaban kasar Hassan Rouhani, ya yi takatsantsan da Amurka, sannan ya bukaci gwamnatin kasar da ta sauke nauyin da ke rataye a wuyanta karkashin yarjejeniyar.

Shugaban babban bankin kasar, Valiollah Seif, ya ce an soma shirin tura kadarorin da aka saki na dala biliyan 32 zuwa kasar.

A ranar Asabar ne aka dage takunkumin da aka kakabawa Iran, wanda hakan na nufin za ta fara sayar da man fetur dinta a kasuwannin duniya.