'Yan majalisa na so a kashe masu cin hanci

Image caption 'Yan majalisar sun ce kashe masu karbar hanci ne kawai mafita a Najeriya.

A Najeriya, wasu 'yan majalisar wakilan kasar sun ce za su goyi bayan duk wani yunkuri na samar da dokar da za ta tanadi hukuncin kisa ko kuma yanke hannu ga duk mutumin da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a kasar.

Hakan na zuwa ne a lokacin da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a kasar ke ci gaba da binciken wasu 'yan kasar da ake zargi da karkatar da makuden kudaden gwamnatin a shekarun da suka gabata.

Honourable Yakubu Umar Barde na jam'iyyar PDP, shi ne mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a Majalisar wakilan Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa daukar matakan hukuncin kisa a kan aikata cin hanci da rashawa zai taimaka wajen magance matsalar cin hanci a Nigeria.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar cin hanci da rashawa dai na daga cikin kalubalen da Najeriya ke fuskanta, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin hukunta duk mutumin da aka samu da laifin karbar hanci da rashawa.