Nijar: Masu Otal na kukan rashin agaji

Shugaba Muhammadou Issoufou
Image caption Zanga-zangar ta janyo asarar dukiya.

A Jamhuriyar Nijar,kungiyar masu Otal-Otal da gidajen shakatawa, ta koka game da rashin biyan mambobinta diyyar dimbin asarar da suka yi sakamakon zanga-zangar kin jinin jaridar Charlie Hebdo.

Wasu matasa ne suka yi wannan bore Damagaram da Yamai, a ranakun 16 da 17 ga watan Janairun bara.

Kungiyar ta ce wasu daga cikin 'ya'yanta na cikin bakar wahala, amma gwamnatin ta ce ba ta manta da su ba.

A ranar Litinin ne dai kungiyar ta yi wannan sanarwar domin tuna wa gwamnatin Nijar alkawarin da ta dauka na tallafa wa 'ya'yanta.

An dai yi asarar dimbin dukiya a lokacin zanga-zanga a a Jamhuriyar Nijar.