Sarah Palin na goyon bayan Donald Trump

Sarah Palin Hakkin mallakar hoto a
Image caption Mis Palin na da farin jini a Amurka.

Tsohuwar mataimakiyar dan takarar shugaban kasar Amurka a shekarar 2008, Sarah Palin, ta nuna goyon bayanta ga dan takarar jam'iyyar Republican a zabe mai zuwa Donald Trump.

Wannan na daga cikin goyon baya na musamman da attajirin dan takarar karkashin jam'iyyar Republican ya samu.

Abin alfahari ne dai mutane irinsu Mis Palin su nuna goyon baya ga Mista Trump saboda duk da ta bar siyasa, har yanzu ta na da farin jini da karfin fada aji ga al'umar Amurka.

A sanarwar da ta fitar ta goyon bayan Mista Trump a hukumance, Mis Palin ta ce dan takara ne da shirya tsaf dan yaki da kungiyar IS.

Kuma zuciyarsa cike ta ke da son cimma muradun Amurkawa da ci gabansu.

Mista Trump ya ce abin alfahari ne a gare shi, mutane kamar Mis Palin su nuna ma sa goyon baya.