Wani dan Shi'a ya soki kasashen yamma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mohammed al-Nimr ya ce Amurka da Biritaniya na kawance da Saudiyya ba tare da la`akari da yadda dangantakar za ta shafi al`umominsu ba.

Dan malamin Shi'ar nan na kasar Saudiyya da aka kashe, Nimr al-Nimr, wato Mohammed al-Nimr ya soki kasashen yammacin duniya, yana cewa sun gaza wajen yi wa Saudiyyar matsin-lamba dangane da wasu manufofinta.

A wata hira da BBC, Mohammed al-Nimr ya ce Amurka da Biritaniya na kawance da Saudiyya ba tare da la'akari da yadda dangantakar za ta shafi al'umominsu ba.

A cewarsa, babu wani bambanci tsakanin akidar Wahabiyancin da ake yi a kasar Saudiyya da akidar da 'yan kungiyar IS ke dogaro da ita wajen yin aika-aikarsu.

Ya ce, "Ga misali, gwamnatin Saudiyya na goyon bayan Wahabiyanci, wadda akida ce da ba ta da banbanci da ta kungiyar IS. Ya kamata mu dinga tunawa da hakkin bil'adama. Mu dinga duba muradan Birtaniya da Amurka idan tafiya ta yi nisa".

Kisan da aka yi wa Sheikh Nimr al-Nimr dai ya bakanta ran mabiya akidar Shi'a a duniya, duk kuwa da cewa kasar Saudiyya ta ce ta kama shi da aikata ta'addanci.