"Rikicin Iraki ya kashe mutane 18,800"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dinkin duniya ta ce mayakan kungiyar IS sun aikata kashe-kashen kare-dangi.

Majalisar dinkin duniya ta ce rikicin da aka yi a Iraki a tsakanin ranar daya ga watan Janairun shekarar 2014 zuwa 31 ga watan Oktoban shekarar 2015 ya yi sanadiyar mutuwar farar hula kimanin 18,800.

Wani rahoto da majalisar ta fitar ya ce kimanin mutane miliyan uku da dubu dari biyu rikicin ya raba da muhallansu a tsawon lokacin.

Rahoton ya zargi kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci, wacce ke rike da yankuna da dama na kasar, da aikata laifukan take hakkin bil adama da yin kashe-kashen kare-dangi.

Rahoton ya kara da cewa su ma dakarun tsaron Iraki da 'yan bindiga da kuma mayakan Kurdawa sun aikata laifukan cin zarafin jama'a.

Babban jami'in majalisar dinkin duniya kan kare hakkin dan adam, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce rahoton "ya nuna irin halin da 'yan gudun hijirar Iraki da ke son guduwa zuwa Turai da sauran yankunan duniya ke ciki. Wannan shi ne irin bala'in da suke fuskanta a kasashensu".