Kotu ta bayar da umarni a kai mata Dasuki

Image caption Ana zargin Sambo Dasuki da halatta kudin haramun.

Wata kotun tarayya da ke birnin Abuja na Najeriya ta umarci lauyoyin gwamnatin tarayya da su tabbata an kai tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki kotu a zaman da za a yi na gaba don ci gaba da yi masa shari'a.

Kotun -- karkashin jagorancin mai sharia Adeniyi Ademola -- ta bayar da umarnin ne a zamanta na ranar Laraba, sakamakon rashin kawo Kanar Dasuki a gabanta.

Lauyoyin da ke kare Kanar Dasuki dai sun ce jami'an tsaro sun hana iyalinsa ganawa da shi.

Kotun ta kuma sanya ranar goma sha shida ga watan Fabrairu domin yanke hukunci kan bukatar gwamnatin tarayya ta a gudanar da shari'ar Kanar Dasuki cikin sirri, ko da ya ke lauyoyinsa na adawa da hakan.

Ana tuhumar Kanar Dasuki ne da laifin mallakar makamai ba bisa kaida ba, da kuma halatta kudaden haram.

Sambo Dasuki na fuskantar wasu shari'iun a gaban wasu kotunan na daban, bisa zargin sace kudaden da suka kai $2.1bn wadanda aka ware domin sayen makamai na yaki da 'yan Boko Haram.