Ana zanga-zanga kan karin farashi a Ghana

Image caption Dumbin mutane na zanga-zanga kan karin farashi a Ghana.

Mutane da dama a Ghana sun fita zanga-zanga a Accra, babban birnin kasar, a ranar Laraba.

Mutanen suna zanga-zangar ne don nuna adawa da karin kudin wuta da ruwa da na man fetur da aka yi.

Suna dauke da kwalaye da aka yi rubutu daban-daban kamar su, "Talauci shi ne babban tashin hankali, da kuma "'Yan siyasa ku ceto mana rayuwarmu ta gaba."

An dai kara farshin kudin ruwa da kashi 67 cikin 100 a watan Disambar 2015 yayin da kudin lantarki kuma aka kara shi da kashi 59 cikin 100.

Masu zanga-zangar kuma na korafi kan kaddamar da sababbin kudaden haraji da kuma kari a kan wadanda dama ake biya.

Kungiyar kwadago ta kasar ce ta shirya wannan zanga-zanga, sannan kuma akwai shirin fara yajin aiki ranar Alhamis da Juma'a.

kan karin kudin wuta da ruwa da na man fetur da aka yi.

Mutane na dauke da kwalaye da aka yi rubutu daban-daban kamar su, "talauci shi ne babban tashin hankali, da kuma "'Yan siyasa ku ceto mana rayuwarmu ta gaba."

An dai kara farshin kudin ruwa da kashi 67% a watan Disambar 2015 yayin da kudin lantarki kuma aka kara shi da kashi 59%.

Masu zanga-zangar kuma na korafi kan gabatar da sabbin haraji da kuma kari a kan wadanda dama ake biya.

Kungiyar kwadago ta kasar ce ta shirya wannan zanga-zanga, sannan kuma akwai shirin fara yajin aiki ranar Alhamis da Juma'a.