Ayatollah ya yi tir da kona ofishin Saudiyya

Image caption Jagoran addinin Musulunci na Iran Ayatollah ya ce bai ji dadin harin da aka kai ofishin jakadancin Saudiyya a kasarsa ba.

Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi Allah wa-dai da harin da aka kai ofishin jakadancin Saudiyya da ke Tehran a baya-bayan nan.

Ayatollah ya ce duk da cewa ba zai yi mummunar sukar matakin da matasa suka dauka na yin zanga-zangar ba, amma kuma dole ne ya fada cewar konaofishin bai dace ba.

Ya ce harin abu ne mara kyau, kuma al'amari ne da ba zai yi wa Iran da ma Musulunci dadi ba gaba daya.

Masu zanga-zangar sun kona ofishin jakadancin Saudiyyan ne don nuna adawa da kashe wani Malamin Shi'a da Saudiyyar ta yi.

Al'amarin ya jawo tabarbarewar dangantaka tsakanin Saudiyya da Iran.