Yaron da ya yanke hannunsa saboda son Annabi

Wani matashi a kasar Pakistan, ya sare hannunsa domin ya nunawa mutane cewa yana matukar kaunar manzon Allah (SAW)

Wakilin BBC, Urdu's Iram Abbasi, ya je wani kauye da ke lardin Punjab domin gano dalilin da ya sa wani yaro ya sare hannunsa bayan an zarge shi da yin ridda a bainar jama'a.

Akwai yiwuwar masu karatu ba za su ji dadin wasu daga cikin abubuwan da za su karanta a labarin ba.

"Me ya sa zan ji zafi ko wani tashin hankali a kan yanke hannun da na daga saboda Annabi Muhammad S.A.W?"

Wadannan su ne kalaman Qaiser, wanda ba sunansa na gaskiya ba ne, wanda ya sare hannunsa na dama a 'yan kwanakin da suka wuce saboda ya yi imanin cewar ya yi ridda.

'Yan kauyensu Qaiser da dama sun yi tir bayan wani Malami ya zarge shi da ridda, abin da ya sa Qaiser yanke hannunsa domin ya tabbatar da soyayyarsa ga Annabi Muhammad S.A.W.

A ranar 11 ga watan Janairu ne Qaiser ya ziyarci taron maulidi a masallacin da ke kauyensu da ke arewa maso gabashin Punjab.

A wurin taron ne Malamin da ya tarbi mutanen da suka halarci maulidin ya tambayi cewa "Wa ye ke kaunar Annabi Muhammad S.A.W?" Sai duk suka daga hannayensu.

Sai ya kuma tambayar wanene a cikinku bai yarda da koyarwar annabi Muhammad S.A.W. ba? Ku daga hannayenku! Sai Qaiser ya daga hannusa saboda bai ji tambayar da malamin ya yi ba.

Daruruwan mutanen da ke wurin sun ga lokacin da ya daga hannunsa, nan take Malamin ya zarge shi da yin ridda abin da ya sa Qaiser ya koma gida ya sare hannunsa domin tabbatar da soyayyarsa ga annabi Muhammad S.A.W.

Farooq, wani mai shekara 30, yana daya daga cikin wadanda suka jinjinawa Qaiser.

Da ya je gidansu Qaiser sai ya sumbaci hannunsa da goshinsa, kuma kamar yadda al'ada ta tanadar sai ya saka masa kudi a aljihunsa a matsayinsa na gwarzo.

Babu wani dan kasar ta Pakistan da ya taba daukarwa kansa irin wannan tsattsauran matakin.

Wasu na ganin cewa ya tsira daga fushin jama'a ganin cewar Pakistan kasa ce da ke daukar tsattsaurar mataki a kan duk wanda ya yi ridda.

Wannan matakin da Qaiser ya daukarwa kansa domin nunawa mutane soyayyarsa ga annabi Muhammad S.A.W. za su dauke shi a matsayin abin damuwa amma kuma hakan ya nuna yadda ake tir da ridda a kasar Pakistan.

Wannan al'amari da ake ganin cewar 'yar hatsaniya ce kadan, ya zama abin da zai sauya rayuwarsa har abada.