Za a kara zafafa kai hare-hare kan IS

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakataren tsaron Amurka Ash Carter, ya ce za a dakatar da yaduwar kungiyar IS a duniya.

Ministocin tsaro na kasashen Yamma da ke taro a Paris sun amince su kara zafafa kai hare-hare kan mayakan IS da ke Iraki da Syria.

Sakataren tsaro na Biritaniya Michael Fallon, ya ce gamayyar kasashen da ke kai hare-haren za ta mayar da hankali ne kan kawar da jagorancin kungiyar IS da abubuwan more rayuwa da suka hada da hanyoyin sadarwa.

Kazalika, sakataren tsaron Amurka Ash Carter, ya ce gamayyar kasashen na da burace-burace uku ne na ruguza kungiyar IS a wuraren da ke karkashin ikonta da suka hada da Raqqa da Mosul.

Mista Carter ya kuma ce, "Za mu dakatar da yaduwar kungiyar a duniya da kuma kare hakkokin al'ummar kasashen."

Ministocin harkokin wajen na kasashe 27 da suka hada da Iraki da sauran kasashen Larabawa da dama za su sake wani taron a Brussels a watan Fabrairu.