An haramta auren wuri a Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kashi daya bisa uku na matan Zimbabwe an musu auren wuri ne.

Kotun kundin tsarin mulki ta Zimbabwe ta haramta aure ga dukkan wanda bai kai shekara 18 ba.

Masu fafutuka sun nuna matukar jin dadi dangane da wannan hukunci da suke ganin wani mataki ne na kawo karshen auren wuri a kasar.

Wadansu amare da aka yi wa auren wuri sun nemi kotun da ta haramta irin wannan auren, suna masu cewa wata hanya ce ta cin zarafin yara wadda ke jefa su cikin halin talauci da wahala.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce kusan kashi daya bisa uku na matan Zimbabbwe an musu aure ne kafin su kai shekara 18.

Ana ganin dai wasu iyayen na yiwa yara auren wuri ne bisa tilas daga shekaru 12 saboda talauci da bin salon al'adu.