Buratai ya umurci sojoji su bayyana kadarorinsu

Hakkin mallakar hoto NIGERIA GOVT
Image caption Manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Babban hafsan sojin kasa a Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya umurci dakarun kasar su bayyana kadarorinsu.

A cewarsa, sojojin kasar na karkashin dokokin ayyukan gwamnatin a don haka wajibi ne su tabbatar sun bi ka'idar bayyana kadara.

Wata sanarwa da kakakin sojin kasar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar ta ce, tuni Buratai ya bayyana kadarorinsa bayan da aka ba shi mukamin babban hasfan sojin kasar.

Wannan umurnin na zuwa ne kwanaki bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a binciki wasu tsofaffin hafsoshin sojojin kasar bisa zarginsu da hannu wajen wawure kudaden gwamnati na sayen makamai.

A cikin tsaffin sojojin da ake zargin, har da tsofaffin manyan hafsoshin sojojin sama da na kasa wadanda su ka yi aiki a karkashin tsohon shugaba, Goodluck Jonathan.