Za a soma shari'ar Ongwen a kotun ICC

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dominic Ongwen tare da kwamandan dakarun Uganda, Kanar Kabango

Kwamandan kungiyar Lord's Resistance Army (LRA), ta Yuganda, zai bayyana a Kotun Miyagun Laifuka da ke birnin Hague.

Dominic Ongwen, wanda aka sace aka kuma horar da shi zama sojan sa kai tun yana yaro, an kama shi ne a Jumhuriyar Tsakiyar Afrika a watan Janairun bara, bayan kwashe shekaru yana buya.

Kungiyar ta LRA tana da mutane fiye da dubu dari, galibi a Yuganda, wadanda ke ikirarin kafa gwamnatin Kiristanci da za ta yi aiki da littafin bayibul.

Ana tuhumar Dominic Ongwen ne da laifuka saba'in, wadanda suka hada da laifukan yaki da na cin zarafin bil adama.

Alkalin ya tsallake abun da aka saba yi na karanta dukkanin tuhumar a gaban kotun, yana mai cewar yin hakan zai dauki kwana da kwanaki ba'a kammala ba.

Ana zargin Dominic Ongwen ne da jagorantar wasu gungun mutane wadanda suka kai samame wasu sansanoni hudu na mutanen da aka tilastawa barin gidajensu a arewacin Uganda.

Masu gabatar da kara sun bayyanawa kotun, wani karo guda inda Mr Ongwen ya umarci mutanensa da su hallaka farar hula sannan su dafa namansu, su kuma cinye. Haka nan kuma ana zargin Dominic Ongwen da sace wasu 'yan mata 'yan makaranta domin yin lalata da su da karfi, da kuma daukar kananan yara 'yan kasa da shekaru 15 domin yin fada a cikin rundunarsa ta 'yan tawaye.

Masu gabatar da karar sun amsa cewar shima kansa Mr Ongwen irin wannan lamari ya faru da shi, inda kungiyar LRA ta kame shi yana da shekaru 10, to amma sun ce bai kamata ayi amfani da wannan a matsayin wata hujja ba ta aikata irin ta'asar da aka yi a karkashin jagorancinsa.

A cikin kwanaki biyar masu zuwa, dukkanin bangarorin biyu - masu da kara da masu kare shi, zasu samu damar gabatar da hujjojinsu a gaban kotun. Daga nan kuma alkalan zasu samu kwanaki 60 inda zasu yi nazari a kan ko akwai isassun shaidu da ya kamata a gurfanar da Dominic Ongwen a gaban shari'a.

Labarin Mr Ongwen dai ya kunshi akasarin abubuwa masu rikirkirtaswa ne a rikicin da ake yi da kungiyar LRA -- watau inda za'a cusawa yaro akidun da zai gaji masu gallaza masa.