Lassa: Kasuwar maganin bera ta bude a Kano

Image caption Likitoci sun gargadi mutane su yi taka tsantsan wajen amfani da maganin kashe Bera.

A Nigeria, kasuwar masu sayar da maganin bera na kara budewa sakamakon cutar zazzabin Lassa da ke kara yaduwa a kasar.

A yanzu haka wasu mutane na cewa suna sayen maganin ne don kashe ko wanne irin bera, ba ma wai sai wanda ke yada zazzabin na Lassa ba.

Masu sayar da maganin beran dai sun ce a yanzu kasuwa ta bude musu, don mutane suna sayen maganin fiye da yadda aka saba a baya.

Wani dan kasuwa da ya dade yana sayar da maganin bera, ya shaida wa wakilinmu na Kano cewa, fiye da shekara 10 da ya yi yana sayar da maganin bera a jihar Kano, wannan karon ya yi ciniki fiye da ko wanne lokaci.

Masana kiwon lafiya sun gargadi jama'a cewa su kiyaye yadda suke amfani da maganin, saboda guba ce da ba Bera kadai take cutarwa ba, har da dan adam.

Ga hotunan da wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana