'Ana zargin Putin da kashe Litvinenko'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Litvinenko ya rasu ne a wani asibiti a London

Wani bincike da aka yi ya gano cewa shugaban kasar Rasha Vladimia Putin ne ya bayar da umarnin kashe tsohon dan leken asirin kasar Alexander Litvinenko, a shekarar 2006 a Biritaniya.

Binciken ya ce ana ganin Mista Putin ne ya sanya hannu kan bayar da umarnin sanyawa Mista Litvinenko guba a shayi saboda wata kullalliya da ke tsakaninsu.

Sakatariyar harkokin cikin gida Theresa May, ta ce wannan kisan gilla ne da ba za a amince da shi ba, kuma keta dokar duniya ce.

Amma ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce binciken yana cike ne da siyasa.

Matar marigayi Mista Litvinenko ta yi farin ciki da rahoton binciken, ta kuma yi kira kan a sanya takunkumi a kan Rasha da kuma haramta wa shugaba Putin tafiye-tafiye.

Mista Litvinenko ya rasu yana da shekara 43 a London cikin shekarar 2006, kwanaki kadan bayan ya sha shayin da aka sanyawa guba.

Kafin mutuwarsa dai, Mista Litvinenko ya kasance mai matukar sukar lamirin gwamnatin Rasha.