An kai hari gabar tekun Somalia

Wani hari da aka kai Somalia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

An kai hare-haren bindiga da motoci shake da boma-bomai a kan wasu gidajen abinci da ke wasu fitattun wuraren shakatawa na bakin teku a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Bom din farko ya tarwatse ne tun da farko-farkon maraice, kuma ba adade ba sai wasu 'yan bindiga suka bayyana a bakin ruwan.

Sashen Somali na BBC ya ce mota ta biyu ta tarwatse ne bayan kamar sa'a guda.

Wata ruwayar dai ta ce akalla mutum uku ne suka mutu, amma ana fargabar cewa yawan mutanen da suka mutun ya fi haka.

Kungiyar Al Shabab ta yi ikirarin kai harin, kuma ta ce har yanzu mayakanta suna cikin gidajen abincin da ke yankin.

Firayim Ministan Somaliya Omar Abdirashid Ali Sharmarke bayyana harin da cewa dabbanci ne.