Matasa sun dau zafi kan rashin aiki a Tunisia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matasan na cike da fushin rashin aikin yi

Rahotanni na cewa ana gwabza fada a birnin Kasserine na kasar Tunisiya, tsakanin dakarun tsaro da masu zanga-zanga da suke neman aiki.

Kwanaki uku kenan ana wannan gumurzu a yankin, wanda har ya yi sanadin mutuwar dan sanda daya.

Tuni dai zanga-zangar ta yadu zuwa wasu garuruwan daban.

A wani yunkuri na kashe wutar rikicin, gwamnati ta yi alkawarin samar da aikin yi ga matasa kimanin 6,000 da basu da aiki a garin Kasserine.

Wannan tashin hankalin dai na tunawa al’ummar garin juyin-juya halin da aka yi a Tunisiya a shekarar 2011, wanda ya yi sanadin kifar da gwamnatin kasar ta wancan lokacin.