Amazon zai samar da aikin yi 2,500 a Burtaniya

Katafaren kamfanin sayar da kayayyaki ta intanet, Amazon ya ce zai dauki ma'aikata na dindindi su 2500 a Burtaniya a wannan shekarar.

Hakan zai sa yawan ma'aikatan kamfanin na Amazon a Burtaniya ya kai 14,000.

Kazalika, kamfanin ya ce zai samar da wasu karin dubban guraben aikin yi a wasu kasashen Turai.

Kamfanin yana zuba jari wajen fadada ayyukansa a kasashen Turai, da suka hada da kara hajoji a runbun kayansa, wadanda aka fi sani da wuraren biyan bukatu.

A yanzu haka, kamfanin na Amazon ya dauki ma'aikata 40,000 a kasashen Turai, sannan a bara, ya samar da karin guraben aikin yi 10,000.

Kamfanin ya ce ya zuba jarin Fam biliyan 11.5 a wasu kadarori a kasashen Turai da kuma wasu harkokinsa tun a shekarar 2010, kuma Fam biliyan 4.6 a Burtaniya ne.

Amazon ya ce zai samar da karin guraben ayyukan yin ne a kafatanin kadarorin hada-hadarsa a Burtaniya.