Burundi: Kwamitin Tsaro da AU na taro

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi
Image caption Shawarar Pierre Nkurunziza ta neman wa'adi na uku ce ta jefa Burundi cikin rikici

Jakadun kasashen da ke da wakilci a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na wani taro da shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka, AU, don tattaunawa a kan rikicin Burundi.

Ana taron ne a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, kwana guda bayan jakadun Majalisar Dinkin Duniya sun gana da shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza, wanda shawararsa ta neman sake darewa kujera a karo na uku ta haifar da tashin-tashina.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Duniya, Samantha Power, ta ce ganawar ba ta yi armashin da ta so a ce ta yi ba.

Mista Nkurunziza ya yi watsi da kiraye-kirayen hawa teburin shawarwari, da ma aikewa da dakarun kiyaye zaman lafiya na AU.