An sake dage shari'ar Dasuki zuwa Fabrairu

Image caption Dasuki na fuskantar shari'a kan hallata kudin haramun

Babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta sake dage shari'ar da ake yi wa Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan sha'anin tsaro.

Alkalin kotun mai shari'a Hussein Baba Yusuf ya dage sauraron karar zuwa ranar hudu ga watan Fabrairu.

Ana zargin Kanar Dasuki ne dai da laifukan da suka hada da karkatar da kudaden sayo makamai fiye da dala biliyan biyu tare da hadin bakin Shu'aibu Salisu da Aminu Baba-Kusa da kuma wasu kamfanoni.

Sai dai Kanar Sambo Dasuki ya musanta zarge-zargen.

A wata shari'ar kan batun zargin da ake tuhumar Dasuki, a ranar Talata ne wata kotun a gabatar da shi gabanta kafin ta ci gaba da shari'arsa.

Lauyoyin da ke kare Kanar Dasuki dai sun ce jami'an tsaro sun hana iyalinsa ganawa da shi.