Iran da China sun bude sabon babi

Shugaba Xi Jinping na China da Shugaba Hassan Rouhani na Iran Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Hassan Rouhani ya yi wa Shugaba Xi Jinping kyakkyawar tarba

Iran da China sun ce sun bude wani sabon babi a gandantakar da ke tsakaninsu.

Kasashen sun bayyana hakan ne yayin ziyara ta farko da wani daga cikin shugabannin kasashen duniya ya kai Tehran tun bayan dage takunkumin da aka kakabawa Iran din mako guda da ya gabata.

Shugaban kasar China, Xi Jinping, da takwaran aikinsa na Iran, Hassan Rouhani, sun amince da wadansu jerin matakai na bunkasa cinikayya da abota ta siyasa.

Mista Rouhani ya kwatanta ziyarar da cewa mai dimbin tarihi ce, sannan ya yi bayani a kan kulla muhimmin kawance.

Mista Xi ne shugaban kasar China na farko da ziyarci Iran a cikin shekaru fiye da goma.

Karin bayani