Yara a Kaduna na dandazo a makarantu saboda abinci

Makarantun Firamare a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na ci gaba da bunkasa sanadiyyar sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar na fara ciyar da dalibai.

Dubban yara ne ke halartar makarantu a jihar, kari ga daliban da ke da rijistar karatu a makarantun.

Jama'a da dama na cire 'ya'yan su daga makarantun kudi da suke halarta suna mai da su makarantun gwamnati don saboda sanarwar ta ciyarwa da kuma bayar da ilimi kyauta.

Har da jami'an agaji na Red Cross ne ke zuwa irin wadannan makarantun don saboda turmutsutu da ke wakana musamman lokacin ba da abinci.

Gwamnatin jihar Kaduna dai na cewa dole daga farko a sami matsaloli to amma sannu a hankali zaa sami sauki.

Wakilinmu Nurah Muhammad Ringim ya halarci wata makarantar firamare da ke unguwar Rigasa domin ganin yadda ake gudanar da shirin.