'Kenya ta san za a kai wa sojojinta hari'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al-Shabaab ta ce ta kashe sojojin Kenya sama da 100.

Wani Janar na sojin Somalia ya yi zargin cewa an gargadi dakarun Kenya da ke kasar a kan yiwuwar cewa kungiyar al-Shabab za ta kai musu hari kwana 45 kafin a kai harin.

Kungiyar dai ta kai harin ne a sansanin sojin kenya da ke Somalia.

Janar Abas Ibrahim Gurey ya shaida wa BBC cewa an gabatarwa da rundunar sojin Kenya kwararan shaidu da ke nuna cewa al-Shabab da ke yankin Gedo na shirn kai musu hari.

Ya kara da cewa dakarun al-Shabab sun yi ta taruwa a yankin gabanin su kaddamar da harin.

Rundunar sojin Kenya dai ba ta ce komai a kan wannan batu ba.

Sai dai Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya yana halartar taron tunawa da sojojin kasar da aka kashe a harin na Somalia, a Nairobi, babban birnin kasar.

Kungiyar Al-Shabab ta ce ta kashe sojojin Kenya sama da 100 a lokacin da ta kai harin, ko da ya ke rundunar sojin Kenya ba ta tabbatar da yawan dakarunta da aka kashe ba.