An gargadi Turai kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Valls ya ce Tarayyar Turai na fuskantar hadari.

Firayim Ministan Faransa Manuel Valls ya yi gargadin cewa al'umar Turai ka iya wargajewa idan ta rungumi dukkan masu gudun hijirar da ke kwarara nahiyar.

A wata hirar da ya yi da BBC, Mista Valls ya ce makomar Tarayyar Turai na fuskantar hadari, sakamakon rikicin masu gudun-hijira.

Ya bayyana shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a matsayin jaruma dangane da tsarinta na rungumar dukkan 'yan gudun-hijira.

Amma ya ce wasu sakonnin da aka samu a cikin wayoyi a sansanonin masu gudun hijira sun isa ishara.