Wakilan MDD sun ziyarci 'yan hijira a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri

Wasu wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu sa ido a kan kare hakkin Bil-Adama sun nuna bukatar yin gyara ga al'amuran tallafa wa matan da aka kubutar daga kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya.

Koda yake, wakilan na musanman su uku, sun yaba da wasu matakan da ake dauka, a lokacin da suka yi rangadi na kwanaki biyar a Nigeria.

Daga cikin gyare-gyaren da tawagar wakilan na Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gano, akwai rashin hukunta masu cin zarafin matan da yara, da kuma kyamar matan da aka kubutar, wadanda 'yan Boko Haram suka taba sacewa.

Jami'an, wadanda suka gana da wakilan gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu, sannan suka ziyarci wasu cibiyoyin da ake tsare wadanda ake zargi da alaka da kungiyar Boko Haram, sun bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da suka kira bayan rangadin nasu.

Sun ce rangadin na su, ya bude musu ido sosai, na sanin halin 'yan gudun hijira ke ciki.