Guguwar dusar kankara ta tsayar da komai a Amurka

Guguwar dusar kankara a Amurka
Image caption Guguwar dusar kankara a Amurka

Guguwar dusar kankara ta mamaye arewa maso gabashin Amurka, inda masana ke hasashen ita ce mafi girma da aka samu cikin shekaru dari.

Karfin zubar dusar kankarar wacce mahaukaciyar guguwa ta haddasa, ya tilastawa hukumomin kafa dokar ta-baci a birnin Washington DC na rufe makaratu da dakatar da harkokin sufuri.

Mahukunta a Birnin New York ma sun ayyana dokar ta-baci kan yanayin, inda aka dakatar da dubannin jiragen sama daga tashi da sauka.

An kuma gargadi mutane fiye da miliyan hamsin cewa a cikin sa'oi kadan zasu fuskanci saukar dusar kankara mai tsananin gaske .