Zaria: An nada lauyan hukumar bincike

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Gwamna Nasir El-Rufai ne ya kafa hukumar binciken a makon jiya

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta nada Yusuf Olaolu Ali a matsayin lauyan Hukumar Bincike a kan Rikicin Sojoji da 'Yan Shi'a a Zaria.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin ta fitar.

Mista Ali ya zama cikakken lauya ne a shekarar 1983, kuma ya zama babban lauyan Najeriya, wato SAN, a shekarar 1997.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin ta Jihar Kaduna ta sanar da mambobin hukumar a karkashin shugabancin Mai Shari'a Mohammed Lawal Garba, shugaban Shiyyar Fatakwal ta Kotun Daukaka Kara.

A watan Disamba ne dai aka yi fito-na-fito tsakanin 'yan Shi'a da sojoji a birnin Zaria, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, aka kuma rushe cibiyar 'yan Shi'ar wacce ake kira Hussainiyya da gidan shugabansu wanda a yanzu yake hannun hukumomi, Shaikh Ibrahim Al-Zakzaky.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ranar Juma'a 29 ga watan Janairu za a kaddamar da hukumar, wacce ake sa ran za ta mika rahoton bincikenta makwanni shida bayan ta fara zama.

Karin bayani