Cutar Zika na neman fin karfin hukumomi a Brazil

Wata jaririya mai fama da cutar Zika a Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata jaririya mai fama da cutar Zika a Brazil

Mahukunta a kasar Brazil sun ce suna fargabar cewa kwayar cutar nan ta Zika da sauro ke yadawa na neman fin karfinsu.

An danganta kwayar cutar da haddasa karuwar jariran da ake haihuwa da tawaya.

Masu bincike sun ce yanayi mai danshi da kuma yadda matsalar tattalin arziki ta shafi bangaren kiwon lafiya sun taka rawa wajen karuwar annobar.

Kwayar cutar ta Zika wacce ta shafi sauran kasashe da dama na Latin Amurka, na kara haifar da damuwa gabanin gasar wasan Olympic da za a fara a birnin Rio de Janeiro nan gaba cikin wannan shekarar.

Jami'an kiwon lafiya na Amurka na kara gargadi ga mata masu juna biyu da su guji zuwa kasashe fiye da 20 na Latin Amurka da suka hada da tsibiran Samoa da kuma Cape Verde.

Kungiyar lafiya ta Duniya WHO ta ce an bada rahoton barkewar annobar cutar Zika din a kasashe goma a Afirka, da Asia da yankin Pacific.