Ana kyamar "matan Boko Haram" —MDD

Image caption Wakilan MDD Dainus Pūras (daga hagu) da Urmila Boola da Maud de Boer-Buquicchio

Wasu wakilan Majalisar Dinkin Duniya na musamman masu sa ido a kan kare hakkin Bil-Adama sun nuna damuwa da yadda suka ce ana kyamar mata ko 'yan matan da 'yan Boko Haram suka taba sacewa.

Daya daga cikin wakilan, Urmila Boola, mai sa ido a kan lamuran da suka shafi bauta, ta ce ta zanta da wata matashiya wacce ta ce danginta sun yi korar kare.

"Na yi magana da wata matashiya 'yar shekara 20 wacce ta haihu lokacin tana hannun 'yan Boko Haram.

"Ta shaida min cewa bayan ta samu ta tsere daga Dajin Sambisa, ta yi kokarin komawa wurin danginta a wajen birnin Maiduguri, inda iyayenta da yarta suke. Amma bayan ta koma wajen yar tata, sai aka ce ita matar 'yan Boko Haram ce saboda haka ba a maraba da ita".

Mis Boola ta kuma ce wajibi ne hukumomi, da sarakunan gargajiya, da kungiyoyin agaji, su hada karfi da karfe don ganin sun shiga tsakani an fahimtar da al'umma cewa ko ma wanne hali wadannan mata da 'yan mata suka shiga ba laifinsu ba ne.

Wannan batu dai na cikin abubuwan da wakilan na musamman na Majalisar Dinkin Duniya—Urmila Boola mai sa ido a kan lamuran da suka shafi bauta, da Maud de Boer-Buquicchio, mai sa ido a kan cinikin kananan yara, da Dainus Puras, mai sa ido a kan hakkokin al'umma na samun kula da lafiya—suka ce suna bukatar gyare-gyare.

Koda yake, wakilan na musanman sun yaba da wadansu matakan da ake dauka don tallafa wa da sake tsugunar da matan da ''yan matan da rikicin na Boko Haram ya shafa.

Karin bayani