Mummunnan dusar kankara a Amirka

Hakkin mallakar hoto Reuters

Amurka ta ayyana dokar ta baci sakamakon iska mai karfi da kuma zubar dusar kankara mai yawa a galibin gabashin gabar kasar.

Lamarin ya haifar da gagarumin tsaiko a harkokin sufurin motoci da jiragen kasa da kuma na sama.

An sami zubar dusar kankara fiye da rabin mita a Washiongton DC a ranar Juma'a kuma masu hasashen yanayi sun ce akwai yiwuwar samun zubar dusar kankarar mai yawa a nan gaba.

Magajiyar garin Washington Muriel Bowser ta yi kira da gaggawa ga jama;a su zauna a cikin gidajensu.

A Kentucky sai da yan sanda suka kafa sansanonin wucin gadi na gaggawa yayin da daruruwan jama'a suka yi cirko cirko sakamakon yawan dusar kankarar a daya daga cikin manyan hanyoyi.

A yanzu guguwar da ke tafe da dusar kankarar ta nausa arewa maso gabas inda ta doshi birnin New York.