Cutar Zika:Mata su guji daukar ciki

Gwajin kwayar cutar Zika a kasar Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwajin kwayar cutar Zika a kasar Brazil

Kasashen Latin Amurka da Caribbean na yin gargadi ga mata da su guji samun juna biyu, saboda fargabar yaduwar kwayar cutar Zika.

Ana dai danganta kwayar cutar Zika wacce sauro ke yadawa da haddasa haihuwar jarirai masu tawaya.

Barkewar annobar cutar Zika a kasar Brazil da ake ganin ita ce ta haddasa yawan haihuwar jariran da nakasar ce dai ta kara iza yin wannan gargadi.

Jami'an kiwon lafiya a kasashen Colombia, da Jamaica, da El Salvador da kuma Ecuador na ta yin kira tare da bai wa mata shawarwari kan su tsahirta samun juna biyu har sai an samu cikakkun bayanai game da yaduwar cutar ta Zika.

Masu rajin kare hakkin mata na sukar lamirin wadannan shawarwari da cewa akasari mata a wadannan kasashe basa samun yanci ko kuma dama game da samun juna biyu.

Kwayar cutar ta Zika wacce ta shafi sauran kasashe da dama na Latin Amurka, na kara haifar da damuwa gabanin gasar wasan Olympic da za a fara a birnin Rio de Janeiro nan gaba cikin wannan shekarar.

Jami'an kiwon lafiya na Amurka na kara gargadi ga mata masu juna biyu da su guji zuwa kasashe fiye da 20 na Latin Amurka da suka da tsibiran Samoa da kuma Cape Verde, inda aka bada rahoton bullar cutar ta Zika.

Sai dai ba a yada cutar ta Zika ta hanyar yin mu'amala ko taba jikin wanda ya kamu da ita.

Kungiyar lafiya ta Duniya WHO ta ce an bada rahoton barkewar annobar cutar Zika din a kasashe goma a Afirka, da Asia da yankin Pacific.