An kashe wani mutum a harin Boko Haram a Yobe

Harin Boko Haram a wani kauye

Rahotanni daga jihar Yobe a yankin arewa maso gabacin Najeriya sun ce wasu da ake jin yan Boko Haram ne sun kai wani hari a garin Babban Gida.

Rahotannin sun ce mutanen garin na Babban Gida sun ce mutum daya ne ya rasa ransa a sakamakon harin, haka kuma an kone gidaje biyu da kuma wani injin nika a harin da aka kai a daren ranar Asabar .

Daya daga cikin mazauna garin da ya tabbatarwa da BBC labarin, ya kara da cewa 'yan Boko Haram din sun kwashe kimanin sa'o'i biyu suna harbe-harbe a garin.

Kawo yanzu dai duk kokarin da wakilinmu yayi na jin ta bakin hukumomi kan wannan hari bai samu nasara ba.

Wakilin namu ya ce ya buga wayar jami' an sojojin da ke da hakkin magana da yawun rundunar sojin Najeriya, amma har yanzu babu wanda ya yarda ya yi magana.

Jihar Yobe na cikin jihohin da Boko Haram ke yawan kai hare hare a Najeriya