Iran za ta sayi jiragen sama 114

Image caption Wani matukin jirgin saman Iran samfurin Airbus, wadanda kasar za ta yi odar irin su daga kamfani Boeing na Faransa.

Iran za ta sayi jiragen sama 114 samfurin Airbus daga kamfanin Boeing na Faransa.

Ministan sufuri na kasar Abbas Akhundi ne ya fadi haka a kafafen yada labaran kasar.

Ministan ya kuma kara da cewa shugaban kasar Hassan Rouhani zai sa hannu a wata yarjejeniyar cinikayya tsakanin Iran da kamfanin kirar jiragen sama na Boeing a wata ziyara da zai kai Faransa ranar Laraba.

A yanzu Iran ta samu damar kawar da tsaffin jiragen samanta, sakamakon dage takunkumin karya tattalin arziki da kasashen duniya suka kakaba mata saboda shirinta na nukilya.

Kasashen yamma sun yi kiyasin cewa Iran na bukatar akalla jiragen sama 400 nan da shekaru goma masu zuwa.

.