An dage bikin Kannywood Awards

Image caption Hatimin walimar bikin Kanywood Award da za a yi a Kaduna a karshen wata a inda za a bayyana jaruman shekara 2015

An dage bikin raba kyaututtuka ga jarumai da kuma fina finan da suka yi rawar gani, watau Kannywood Awards na wannan shekara 2016

A wata hira da BBC ta yi da shugaban gudanar da bikin Dr. Ahmed Sarari ya ce an dage bikin ne saboda janyewar kamfanin MTN daga daukar nauyin bikin na wannan shekara, da kuma bukatar wasu manyan baki da aka gayyata na a daga, domin su samu damar halarta.

Bikin wanda aka shirya za a yi shi a Abuja a karshen watan Janairu, an dage shi har sai wani lokaci nan gaba.

Amma za a gudanar da walimar sanar da wadanda suka lashe kyaututtukan bana a Kaduna a karshen watan nan, kamar yadda aka tsara.

Cikin wadanda suka ci kyaututtuka a bikin na shekarar 2015 sun hada da sadiq Sani Sadiq wanda ya samu kyautar jarumin jarumai, da Hadiza Gabon wacce ta zama jarumar jarumai, da kuma marigayi Rabbilu Musa Dan Ibro wanda ya samu kyautar gwanin barkwanci.