'Mun soma fina-finai da Turanci'

Image caption Mai bada Umarni Falalu Dorayi da mai Shiryawa Abba Al Mustapha, da wasu 'yan wasa da kuma ma'aikata a lokacin daukar fim din 'There is a way' da Turanci

Masu shirin fim a Kano sun dukufa wajen shirya fim da Turanci.

Hakan ya fito fili ne a inda tsaffi da kuma sabbin jaruman fina-finan Hausa suka yi wa garin tsinke yayin da ake hidimar daukar fim din 'There is a way' da Turanci.

A hirar da ya yi da BBC, Abba Al Mustapha wanda ya shirya fim din, ya ce sun shirya fim ne domin nunawa duniya cewa 'yan kanywood sun iya Turanci kuma za su iya yin fina-finan su da harshen.

Kabiru Jammaje wani malamin koyar da Turanci ne ya dauki nauyin Fim din ya kuma tsayin daka wajen ganin an yi turancin yadda ya dace kuma bisa ka'ida, a yayin daukar fim din, a cewar Falalu Dorayi wanda ya bayar da ummarni.

Labarin fim din tsokaci ne akan gwagwarmayar neman ilimi a jami'a da kokarin cimma buri a rayuwa da kuma kalubalen da ake gamuwa da su.

Fim din ya kunshi 'yan wasa irin su Sani Mu'azu da Hauwa Maina wadanda suka yi fice a fina-finan Turanci na Nollywood.

Sauran jarumai a fim din sun hada da Rabiu Rikadawa, da Zainab Booth da Saratu Gidado da Umar Malumfashi da kuma Babballe Hayatu.

'There is a way' zai zamo zakaran gwajin dafi a fina-finan da ake shiryawa daga arewacin Najeriya da Turanci.