Barayin shanu 39 sun tuba a jihar Kano

Image caption Bayayin sun ce sun tuba ne saboda suna jin tsoron haduwa Allah.

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Nigeria ta yi wa wasu barayin shanu afuwa, bayan da suka ce sun tuba da satar.

Mutane 39 da ke yankin Gomo a karamar hukumar Sumaila ne suka mika wuya ga hukumomin, wadanda kuma aka yi musu afuwa a wani biki da aka gudanar a yankin nasu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Muhammad Musa Katsina, ya ce sun bai wa barayin shanu a jihar zabi -- ko dai su mika wuya ko kuma a bi su cikin daji a kama su.

Kusan dukka wadanda aka yi wa afuwar suna cewa sun mika wuya ne saboda tsoron Allah da kuma ganin satar shanun hanya ce ba mai bullewa ba.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya ce daya daga cikin sharuddan da aka gindaya wa barayin da suka tuba, shi ne ba za su sake komawa aikata kowanne irin babban laifi ba.

Hukumomi dai a jihar Kano na fatan wannan mataki na tuba da wasu satar shanu a Kano su ka yi zai taimaka wajen karya kashin-bayan masu satar shanu a jihar, kasancewar da dama daga wadanda suka tuba din, gawurtattun barayi ne da suka addabi jihar.

Masu sharhi dai na fatan mutanen sun tuba ne har zuci, inda suka ce Allah ya sa ba tuban muzuru ba ne.