Kerry: Za a soma tattaunawar zaman lafiya a Syria

John  Kerry Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sakataren Harkokin wajen Amurka

Yayin da fada ya ci gaba a Latakia -- da kuma Lardin Deir al-Zor -- Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce yana da fatan cewar za a soma tattaunawar wanzar da zaman lafiya a Syria cikin mako mai shigowa a Switzerland.

Mr Kerry ya ce ya tattauna a kan hanyoyin kawo karshen rikicin a lokacin ziyararsa zuwa Saudiya.

Har yanzu akwai sauran bambance bambance game da tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta hada.

Mr Kerry dai na yin tuntuba akai akai tare da takwaran aikinsa na Rasha, Sergie Lavrov don kokarin cimma yarjejeniyar da kungiyoyin yan tawaye za su iya shiga sahun tattaunawart wadda za ta hada da gwamnatin Syria da masu mara mata baya Iran da Rasha da kuma Saudiya.